Saturday, 14 October 2017

Nigeria: Majalisa za ta binciki asibitin fadar shugaban kasar



'Yan majalisar wakilan Najeriya za su gudanar da bincike a kan mawuyacin halin da asibitin fadar shugaban kasar ke ciki.

'Yan majalisar sun nuna damuwar cewa duk da irin makudan kudaden da ake ware wa asibitin a kasafin kudin Najeriya , amma ana samun rahoton rashin kayan aiki a asibitin.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta zargi asibitin da rashin kayan aiki a makon da ya gabata, lokacin da ta kai ziyara asibitin da ba ta da lafiya.


Hajiya Aisha, ta ce abin takaici ne yadda idan aka duba halin da asibitin fadar shugaban kasa ke ciki, balle kuma a zo maganar sauran asibitocin kasar da ke jihohi ko karkara.

Mai magana da yawun majalisar, Hon Abdurrazak Namdaz, ya shaida wa BBC cewa, tun daga shekarar 2015 zuwa shekarar da muke ciki, ana warewa asibitin fadar shugaban kasar kudade a kasafin kudin kasar, dan haka ya ce dole a bincika domin gano inda kudaden suka tafi.



Hon. Namdaz ya ce wani kwamiti na musamman ne aka bawa wuka da naman gudanar da bincike a kan inda kudaden kula da asibitin fadar shugaban kasar suka shiga.

Dan majalisar ya ce nan ba da jimawa ba kwamitin zai fara aikinsa, kuma da zarar ya kammala binciken ya bayar da rahotonsa, za a sanar da jama'ar kasa komai dalla-dalla.

Blogger
Disqus
Pilih Sistem Komentar Yang Anda Sukai

No comments