Mutane 19 su ka mutu sanadiyyar wani hadarin mota da ya faru a daidai Lambun Garban Bichi, kan hanyar Kano zuwa Katsina.
Kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa na jihar Kano, Kabir Daura ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN haka.
Hadarin inji Daura, ya ritsa da fasinjoji 34 wadanda ke cikin mitocin haya biyu, C20 bas da kuma Fijo J5, inda nan take mutane 18 su ka kone kurmus, yayin da na cikon 19 ya mutu a asibitin garin Bichi.
Ya ce sauran fasinjoji 15 kuma sun samu raunuka, kuma aka garzaya da su asibitin garin na Bichi.
Daura ya ce motocin biyu taho-mu-gamu su ka yi. Ya kuma danganta wannan hadari da gudun tsiya, gaggawa da kuma wuce mota a inda doka ta hana direba ya yi aron hannu ya wuce motar da ke gaban sa.
Sunday, 10 September 2017
Mutane 19 sun rasa rayukansu a hadarin mota a Kano

Tags
Artikel Terkait
- Clicknaij Tech blog Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya nisanta kan sa daga wani ka
- Gwamnatin jihar Lagos da ke Najeriya ta ce tana samun karin rahotannin da ke nuna m
- Kungiyar Malaman Jam'i'o'i ta Kasa, ta amince da yarjejeniyar da ta cimma a zamanta da gw
- 'Yan majalisar wakilan Najeriya za su gudanar da bincike a kan mawuyacin halin da asibi
- Dan wasan Real madrid Cristiano Ronaldo ya samu karuwa cikin jerin motocin da ya tara mas
- Kungiyar ‘Yan Jarida Mata, reshen Jihar Filato sun gudanar da zanga-zangar nuna dam
Newsletter
Berlangganan artikel terbaru dari blog ini langsung via email
Blogger
Disqus
Pilih Sistem Komentar Yang Anda Sukai
Subscribe to:
Post Comments (Atom)