‘Yan sandan Laken Asirin kasar nan, SSS sun taba zurara tsabar kudi a cikin asusun Adulrashid Maina, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar.
Hakan ya nuna cewa an dade ana harkalla tsakanin Maina da kuma jami’an SSS. Dama kuma a ranar Alhamis da ta gabata PREMIUM TIMES ta bayyana yadda jami’an na SSS ke ba shi kariya, watakila don kada EFCC su kama shi.
A halin yanzu dai Maina ya cika wandon sa da iska, tun bayan da EFCC suka bayyana cewa suna neman sa, bayan Shugaban Kasa ya bayar da umarnin a kore shi daga aikin da aka maida shi a asirce.
Wani rahoto na musamman da aka gudanar ya tabbatar da cewa Maina ya yi kaurin suna wajen amfani da wani dan’uwan sa ma’aikacin banki mai suna Khalid Ali Biu, ya bude asusun ajiyar kudi da sunan Cluster Logistics Limited a bankin Fedility. An yi wannan harkallar ce a cikin 2011.
Wani abin mamaki shi ne, Khalid ma’aikacin Fedility ne, sannan kuma ya na daya daga cikin daraktocin wannan kamfani na bogi.
Wani bincike kuma ya tabatar da cewa tsakanin 2011 zuwa 2013, an dura zunzurutun kudi a cikin asusun har naira miliyan 500.
Baya ga wanan an kuma gano cewa an rika cirar tsabar kudi ne daga asusun, wadanda akasari duk daloli ne aka rika cira. Sannnan kuma a cikin asusun ne SSS duka dura wa Maina naira milyan 152.
An kuma gano cewa a baya EFCC ta nemi ta boye wannan asarkala da SSS suka yi domin su rufa wa SSS asiri.