Thursday, 26 October 2017

Na tuba, a yafe mini” Rahama ta roki MOPPAN



Shahararriyar ‘yar wasan fina-finan Hausa Rahama Sadau ta roki kungiyar MOPPAN da ta tausaya mata ta maido ta farfajiyar Fina-finan.

Rahama ta fadi haka ne a wata wasikar tuba da ta rubuta wa kungiyar cewa ta yi nadama kan abinda tayi awancan lokacin.

An kori Rahama Sadau ne daga farfajiyar fina-finan Hausa saboda wani bidiyon waka da tayi da wani mawakin garin Jos mai suna Classique in da ta rungumeshi wanda hakan ya saba wa dokar duk wani dan wasa a farfajiyar Kannywood.

Yanzu dai ta fito fili don rokon a yafe mata.

“Ni halittar Allah ce wanda za ta iya aikata kuskure ko yaushe sannan kuma ni ‘ya ce mai laifi wanda ke shirin gyara abubuwan da nayi ba daidai ba. Ina rokon abokan aikina, da mambobin kungiyar masu MOPPAN, da da masoya na da suyi hakuri da ni su yafe min.

Da gidan jaridar PREMIUM TIMES HAUSA ta zanta da Salisu Mohammed, sakataren kungiyar MOPPAN ya tabbatar da mika wasikar hakan ga kungiyar daga Rahama Sadau.

” Lallai Rahama ta mika wa kungiyar wasikar tuba daga abubuwan da ta aikata a baya ga kungiyar da masoyanta, amma duk da haka sai kungiya ta zauna ta duba wasikar da kuma duba irin abubuwan da tayi ta aikatawa da fadi bayan an kore ta game da kungiyar da farfajiyar fina-finan Hausa sannan ta fitar da matsaya daya.

Blogger
Disqus
Pilih Sistem Komentar Yang Anda Sukai

No comments